Looking For Anything Specific?

Yadda Zaka Bude Page A Blogger | Hausatechs.com

Assalamu alaikum masoya barka da warhaka dafatan kuna lafia yau zamuyi bayani mai muhaimmanci akan yadda zaka iya bude Page A Blogger.
Yadda zaka bude page a blogger
Blogger Page
Wato Blogger itace website kamar yadda mukayi bayani a baya idan baka san ma'anar blogger ba kakaranta Post dinmu na baya Yadda Zaka Free Website A Blogger zaka fahimci menene Blogger. 

              Menene Page A Blogger 
Page Shine Shafi a Hausa ana amfani dashi a blogger domin ajiye wadansu bayanai masu muhimmanci kamar idan inaso in bayyana kaina ni mai website ana amafani da Page mai suna About Me wato game da ni domin bayyana kanka domin masu shigowa website dinka susamu gamsuwa dakai sannan akwai abubuwa da ake bude Page dominsu a blogger Wanda anan gaba kadan zaku ganesu. 


Kuma Page yana da matukar amafani a blogger domin akwai wadansu Page guda 4 wato About Me, Contact Us , Privacy Policy, Disclaimer, Wadannan Page dana lissafa suna da amafani sosai a cikin wadannan Page zaka bayyana wanene kai da kuma kaidar website dinka da kuma yadda za a iya haduwa dakai ta Waya Ko aika Sako sannan zaka iya bayyana dokoki da kaidodi na website dinka.


Wadannan Page Guda 4 dasu website dinka zaicika domin wani idan baiga wannan Page 4 ba bazai yadda dakaiba Wanda yakamata ace duk masu shigowa blog dinka to sun yadda dakai domin hakan zai iya jawo wani yabaka Talla domin bunkasa kasuwancinsa ko wani dayake bukatar ya bunkasa, yaznu zan nuna muku yadda zaku bude Page A Blogger.

Karanta Wannan>> Yadda Zaka Dora Template A Blogger.

Dafarko kashiga Blogger.com kayi Sigh In  da gmail daka bude blogger dashi zai kawoka Shafi kamar wannan.


Yanzu kashiga blog dinka sai kaduba gurin da aka rubuta Page Zaka ganshi A abubuwan dake cikin blogger amma gashi nayi alama akansa yadda zaka gane.


Sai kaduba gurin da aka rubuta New Page Sai kashiga kamar yadda zakaga nayi alama akansa.


Zai bude maka shafi kamar wannan to anan zaka bude shafinka nafarko asama an rubuta Title ma'ana Lakabi wato kasaka sunan Page dakake son budewa sannan sai wannan dakaga nayi alama Ta 2 to anan zaka rubuta abin da shafinka zai kunsa,

Idan ka gama rubuta abin dakake son shafin yanuna sai kadanna Publish Zaka ganshi Asama kamar yadda shima nayi masa alama yadda zaka gane.


Idan kadawo asalin cikin blog dinka sai kaduba inda aka rubuta Page Zaka ga shafin daka bude kamar yadda zaka gani a wannan hoto.

Iyakar abin dazan iya kawo muku kenan akan yadda zaku bude Page a blogger sai kujira a Post nagaba domin zuwa da wani Abu mai muhimmanci kada kumanta duk mai son website kamar Hausatechs.com na sayarwa zai iya samu kawai kaneme mu ta wadannan hanyoyi Facebook Click Here Instagram Click Here Watsapp 07066870719

Idan kaji dadin Wannan Post Kataima Kayi Sharing Zuwa Wasu Gurare Mungode.

                 Please Share Our Post 

Post a comment

0 Comments