Looking For Anything Specific?

(MTN TRANSFER CODE) Yadda Zaka Yi Airtime / Credit Transfer Alayin MTN

Kana Da layin MTN kuma kana son kasan Yadda ake tura kudi daga wani layi zuwa wani ? To kazo inda yadace domin idan kana biye dani yau zaka koyi Yadda Zaka Yi Transfer Airtime Alayi MTN,  Muje Zuwa.


MTN Transfer Airtime Code, Yadda Zaka Yi Transfer Alayin MTN


Kamfanin kiran waya na MTN sun fitar da wani tsari mai suna Share N Sell wannan tsari yana bada dama ga masu amfani Da MTN su tura Airtime/Credit daga layinsu zuwa wani layi wato TRANSFER, sai dai mutane dadama basu san yadda ake Transfer alayin MTN ba wanda yau zamu nuna yadda ake yi.Abu nafarko daza kayi idan kana son yin Transfer alayin MTN shine Change Pin wato akwai bukatar kazabi lambobi na tsaro wanda dasu zaka nayin Transfer akoda yaushe, duk layin MTN yana zuwa da Transfer Default Pin sune 0000 idan kana son yin Transfer dole saika chanza wadannan lambobi zuwa wadanda kakeso.


   Yadda Zaka Saita MTN Transfer Pin

Zaka iya amfani da Hanyoyi 2 domin change Pin hanya tafarko itace Text Messages, kana amfani da wayar Android NE kokuma karamar waya kawai kashiga wajen da ake tura sako wato Message sai karubuta kamar haka:- Default Pin New Pin New Pin' Zuwa ga 777. Dalla Dalla:- Wajen Default Pin kasaka 0000 wajen New Pin kasaka Pin Din dakake son chanzawa saika maimaita wato sau biyu ga Misali, Send:- '0000 1234 1234'  to 777. sai katura zuwa ga 777 dafatan kakane.


Duba Wannan>> Yadda Zaka Samu Kyautar 500MB Alayin MTN,


Hanya ta biyu dazaka chanza Transfer Pin, wannan itace mafi sauki kawai zaka danna lambobi NE basai kashiga Text Messages ba ga Misali, *600*0000*1234*1234# sai katura zaka samu sako kamar haka:- "Your Pin Was Changed Successfully" Abin Lura shine wadannan 1234 danake sakawa ina gwadawane zaka iya zabar lambobi wanda kakeso guda 4 amma dai kasani default pin sune 0000 dole sai kasaka su sannan kasaka New Pin Sau biyu kamar yadda nagwada a sama.


         Amfanin MTN Share N Sell

Tsarin MTN Share And Sell kyautane dafarko sai dai  a wannan shekara wato 2019 MTN suna chaji idan kayi Transfer,  idan kana son yin Transfer Naira 50 to dole yakasance akwai Naira 53 alayinka domin MTN zasu chajeka Naira 3 wato Idan zakayi Transfer Naira 100 zasu chajeka Naira 6 dafatan kagane.


Zaka Iya Tura Airtime / Credit Zuwa kowane layin MTN dake Nigeria daga Naira 50 zuwa Naira 5.000 a lokaci guda kuma zaka iya Transfer Naira 10.000 A rana guda, Sannan ka kula da Pin wanda dashi zakanayin kada kamantashi sannan kada kabari wani yasan Transfer Pin dinka.


Wannan Shine Iya Abin Dazan Iya Kawowa Akan Yadda Zakayi Transfer Airtime Alayin MTN, Saidai Idan Akwai Abin Daba Kugane Ba Zaku Iya Rubuta Korafi Akasan Wannan Post Kokuma Kaitsaye Ta Watsapp 07066870719 Kokuma Ta Shafinmu Na Facebook Click Here. Mungode..


               Please Share Our Post 

Post a comment

0 Comments