Contact Form: Yadda Zaka Bude Contact Us Page A Blogger | HausaTechs.Com

Contact Form: Yadda Zaka Bude Contact Us Page A Blogger | HausaTechs.Com


Kamar yadda muka saba cikin kawo muku yadda ake bude website a blogger cikin sauki to yau insha Allah zamu kawo muku yadda zaku bude Contact Form Da Contact Us page A blog dinku.                  Menene Contact Us ?

Contact Us page wani shafi NE da ake  budeshi a website domin bawa masu shiga damar Kira ko tura Sako,  wato Idan masu shiga blog dinka sukayi niyyar aika maka sako   zasu shiga Contact Us page domin samun hanyar yin hakan,Idan suka shiga zasu samu wajen saka Suna da Email Address  sannan kuma zasu rubuta sakon dasuke so su aika idan suka tura kaikuma zakaga wannan Message yashiga Gmail Da kabude Blog dinka dashi, zakuma kaga wanda yaturo maka da sunansa.Sannan kada kumanta muna muku jagoranci akan Yadda Zaku Samu Kudi A Internet da Blogger wannan page daza mubude yana cikin page guda 4 wanda dole saidasu Google Adsense zai karbi Blog dinka.


Duba Wannan>> Yadda Zaka Bude Website Ko Blog A Blogger         Yadda Zaka Bude Contact Us

Idan kana son bude contact us page sai kayi Sign In a Blogger.Com wato kabude shafin blogger sannan kaduba inda aka rubuta Pages Idan kashiga Pages sai kaduba inda aka rubuta New Page Kamar Dai haka:-Idan kabi abin danace a wannan photo dake sama wato kashiga Pages sai kadanna inda aka rubuta New Page zaka wani shafi kamar haka


Idan shafin dake sama yabude maka zakaga nayi alama babba asama wato inda aka rubuta Page Tittle agurin saika rubuta Contact Us inda kuma nazagaye da aka rubuta HTML sai ka danna gurin idan kasamu wasu rubutu agurin dana rubuta Paste Code Here to kagogesu idan kuma baka samuba sai kasaka wannan Code dazan baka dake kasa Kayi Copy Dinsu Gabadaya Kasaka A Inda Na Rubuta Paste Code Here gasu Akasa.👇
Idan kayi Copy Code dake sama kasaka a inda na rubuta Paste Code Here kamar yadda nafada abaya sannan  sai kaduba gurin Settings yana gefen hagu a blogger gashi A photo dake kasa A wannan shafi abu 3 zakayi idan kadanna alamar Settings zaka ganta A wannan shafi daga gefen hagu sai kadanna inda aka rubuta Don't Allow kamar yadda nazagaye gurin A photo dake sama sannan sai kadanna inda aka rubuta Done sai kuma kaduba inda aka rubuta Publish shima nazagaye shi da Jar Alama shikenan kagama bude Contact US page A Blogger.
Yanzu kabude Contact Us page sai dai kuma wannan page daka bude yanzu koda antura maka sako bazai shigaba dole sai kabude Contact Form page wanda shine mahadin Contact Us page shima kuma yanzu zamu nuna yadda ake budeshi.


Yadda Zaka Hada Contact Form Da Contact Us A Blogger

Yanzu sai kadawo Blogger Homepage sai kaduba inda aka rubuta Layout sannan sai kaduba inda aka rubuta Sidebar akasan sidebar akwai inda aka rubuta Add Gadget gasu A photo
Idan kashiga Add Gadget zakaga wasu jeri dayawa acikin wadannan jerin sai kanemo inda aka rubuta Contact Form sai kadanna wannan alamar + akarshen gurin dana zagaye a photo dake kasa Idan kadanna alamar + zakaga wannan shafin 


Idan shafin dake sama yabude maka sai kadanna inda aka rubuta Save shima nazagaye gurin shikenan kabude Contact Form a Blogger. 
Yanzu saura mai yarage? shine yadda zaka boye Contact Form Page a blogger tunda ana bukatar Page guda 1 NE amatsayin Contact Us to dole saika boye Contact Form yadda idan aka shiga blog dinka iyakar Contact Us Page za a gani. 


Yadda Ake Boye Contact Form A Blogger

Idan Kana Homepage na blogger sai kaduba gurin da aka rubuta Layout sannan kaduba inda rubuta Theme Designer ko Template Design yadanganta da yanayin template dinka gashi a photo 


Idan kashiga Theme Designer sai kaduba gurin da aka rubuta Advanced sai kashiga gashi kamar haka:-


Idan kashiga Advanced zakaga inda nazagaye wani guri wato Add CSS sannan zakaga inda na rubuta Paste Code Here sai kasaka wannan dazan baka.


Inda na rubuta Paste Code Here sai kasaka wannan Code dake kasa gasu akasa👇
Idan kayi Copy Code dake sama sannan kayi Paste dinsu A inda nanuna A sama sai kaduba inda aka rubuta Apply To Blog sai kadanna zakaga yayi Saved na Code din daka saka sannan sai kadanna Back To Blogger zaka ganshi nazayeshi A wannan photo


Idan kana so kagwada cewa ko kaboye Contact Form zaka iya danna View Blog yanzu baza kaga Contact Form ba, tunda kaboye Contact Form yanzu saura Contact Us Page zaka iya shiga kagwada tura sako amma kayi amfani da wani Gmail banda wanda kabude blog din dashi zakaga sako yashiga Gmail dinka daka bude blog dinka dashi.


Jan hankali shine zaka iya sanya Contact Us Page aduk gurin dakake so a blog dinka amma a shawarce kasanya shi a Footer zaka iya duba Footer idan kashiga Layout sannan katafi can kasa karshen kasa nanne footer idan kana son saka Pages agurin sai kadanna Add Gadget zaka saka duk abin dakakeso. 


Iyakar darasinmu kenan akan Yadda Zaka Bude Contact Us Page A Blogger, Sai Kujira Darasi Nagaba Sannan Idan Baku Saniba Muna Da Video Training Yadda Zaka Bude Kyakkywan Blog A Blogger Daga Farko Har Matakin Yadda Zaka Samu Kudi Cikin Kwana Bakwai Zaka Iya Bude Kayataccen Blog A Blogger Zaku Iya Sayen Blogger Video Training Cikin Farashi Kankani.


Jaku Iya Join Da Shafin HausaTechs.Com Na Facebook Click Here Kokuma Zaku Iya Magana Damu Kaitsaye Da Wannan Number 07066870719 Kokuma Sakon Watsapp, Idan Wannan Post Yayi Maka Amfani Don Allah Katura Zuwa Wasu Gurare.  Mungode.

                Please Share Our Post 

Post a comment

2 Comments