Data Reseller - Yadda Ake Kasuwancin Data A Internet > VTU Recharge Card

Data Reseller - Yadda Ake Kasuwancin Data A Internet > VTU Recharge Card


Nasan kunsha ganin post din dayawa a Facebook, Watsapp, Twitter  ko Instagram,  Yadda zaka saro Data daga wani kamfani kasayar domin samun riba.


Wannan kasuwanci babu shakka A wajen samun kudi dakuma babbar riba, Wanda yau darasinmu shine akan Yadda ake kasuwancin data a internet ko VTU recharge card.


Menene Data Reseller? 


Idan zanfada maka atakaice data reseller yana nufin Mai Tallan Data, Wato akwai manyan website dasuke sayar da data akan farashin sari  masu yi musu Talla susamu wani abu.


Wadannan website suma suna samo Data daga ainihin babban kamfanin kiran waya ne kamar MTN, Airtel, Glo, 9Mobile domin susamu riba, Saidai su suna samun Data ko MB cikin farashi kankani wanda kaikuma zasu baka Talla aciki kaima zaka samu rabonka.


Wacce Riba Ake Samu A Data Reseller? 


Yadanganta da yadda kaga zaka iya sayarwa domin  zaka iya samun N100 aduk 1GB daka sayar, Idan kasayar da 5GB kasamu N500 Wani lokacin har sama dahaka domin su zasu baka a farashin sarin NE kaikuma sai yadda kaga dama zaka sayar da ita.


Acikin wannan post zan nuna maka yadda zaka shiga wannan kasuwanci da yadda zaka sayar da Data domin samun babban kudi, Domin wannan bayani yanada Muhimmanci sosai saboda wasu sai kabasu kudi dasu bude maka wannan sirrin amma kai yau zan gaya maka Kyauta.Ina so kasan cewa wannan Business ana samun kudi dashi sosai a internet domin akwai masu samun N50000 cikin kwana 30 (Wata Daya) wasu sama da haka,  Kuma kasuwanci ne wanda ko baka da Website Ko Blog zaka iya yinsa.Abubuwan Dazaka Bukata Kafin Kafara Data Reseller


  • Laptop or Android Phone
  • Your Payment Option ( ATM or Mobile Banking)
  • Data Reseller Pack
  • Money To Start Business

Idan kana bukatar fara wannan kasuwanci zaka mallaki Laptop ko Wayar Android kuma dole kasamu layi mai Data ko MB domin ana wannan Business Online ne, Zakuma katanadi kudi wanda kake son farawa dashi (Zaka Iya Farawa Da N1000). Sannan zaka nemi ATM Card domin sayan Data daga wadancan kamfani dana fada abaya.


Zaka sayi Data Reseller Pack a wajesu domin kafara sayarwa,  Wato zaka saka kudi a Wallet dinka zaka sayi Data Pack kamar 2GB, 5GB, 10GB dadai sauransu idan kasayar sai kasamu riba.


Akwai website dayawa dasuke sayar da Data Reseller Pack amma yanzu zamuyi amfani da SUB9JA wanda yayi fice sosai wajen wannan kasuwanci, Kuma anjima ana amfani dashi wanda hakan  yake nuna cewa lallai Sub9ja suna da inganci wajen Data Reseller Pack.Duba Wannan>> Yadda Zaka Samu Kyautar 500MB Alayin MTN


Yadda Zakayi Register A Sub9ja Domin Data Reseller

Kashiga wannan Address din Click Here To Register  zaka samu kanka a sub9ja website inda zaka saka abubuwan da ake bukata domin yin register.


Idan kashiga wannan guri zaka samu inda zaka saka Details dinka domin yin Register kamar sunanka da sunan mahaifi, Email Address, Password,  dadai sauransu gashi anan


Idan kagama saka details dinka aqarshe zaka samu inda aka rubuta  Check Box To Agree To Terms kataba gurin sannan sai kadanna Register  shikenan kabude Sub9ja Account.


Tunda kayi register yanzu zaka samu kanka a Sub9ja Dashboard sai kadanna inda nanuna da arrow kamar haka 


Idan kadanna inda nanuna maka asama zaka samu jerin abubuwa daza kayi a wannan website sune :-

Massage 
Fund Wallet 
Airtime to cash
Data Bundle
VTU/Recharge
Cable TV 
Education 
Electricity

Da Sauransu ga jerin wadannan abubuwa a wannan Photo dake kasaAna amfani da Message domin tura sakonni masu yawa a lokaci guda (Bulk SMS). 


Zaka shiga Fund Wallet domin saka kudi a wallet dinka na sub9ja wanda dashi zaka dinga sayen data domin sayarwa dakuma sauran abubuwa.


Zaka shiga Airtime to cash idan kana bukatar canja airtime zuwa kudi, Wato idan kana da airtime a wayarka dakake son sayarwa zaka iya turawa sub9ja su kuma zasu tura maka zuwa Account Bank dinka amma zasu cire wani abu daga ciki.


Zaka shiga Data Bundle idan kana bukatar turawa wani Data (Sayarwa) amma katabatar kasaka kudi a wallet dinka kafin sayar da Data.
Ana amfani da Education domin biyan kudin makaranta kamar Neco, JAM da sauransu,  Sannan idan kana so kabiya kudin wutar lantarki online (Nepa Bill) zaka iya shiga Electricity dakuma sauran abubuwa da Sub9ja yakunsa, Wanda ba lallai sai munyi bayani akansu ba tunda muna magana akan Yadda Ake Kasuwancin  Data Reseller.Yadda Zaka Saka Kudi A Sub9ja Wallet Domin Yin Data Reseller

Idan kana bukatar saka kudi a wallet dinka zaka shiga inda nanuna abaya wato Fund Wallet zakaga wani shafi kamar wannan


Anan zaka saka adadin kudin dakake son sakawa a wallet dinka,  Gashi nayi misali da 2000 sai kadanna inda aka rubuta Select Payment Method zakaga wannan shafin


Sai kazabi inda akace Pay with Debit Card(Flutterwave)  idan kashiga wannan gurin sai kadanna Pay zakaga wannan shafinA wannan shafi zaka saka ATM Card details shine inda aka rubuta Card Number sai saka Lambobi 16 na ATM dinka (zaka gansu ajikin ATM) inda aka saka VALID TILL sai kasaka Expire Date na ATM dinka (zaka gansu ajinkin ATM) inda akace CVV zaka saka wasu lambobi 3 (suna bayan ATM)  sai kadanna Pay NGN2,028 wato zasu cire N28 na Transaction N2000 kuma zasu saka maka a wallet dinka.
Wannan kudi daka saka a wallet dasu zaka dinga sayen data kana turawa mutane,  Wato duk lokacin da wani zai sayi data daga gurinka zaka tura masa su kuma zasu cire adadin kudin datan daga cikin wallet dinka.


Yadda Zaka Sayar Da Data Daga Sub9ja Zuwa Kowane Layi Dake Nigeria

Abaya nanuna abubuwan da wannan website yakunsa aciki akwai data bundle, Yanzu sai kashiga inda aka rubuta data bundle sannan kashiga Buy Databundle gashi kamar haka


Idan kashiga buy databundle zai kaika inda zaka saka number daza katurawa data, Sannan kazabi layin dazaka aikawa datan da kuma adadin dakake son turawa gashi anan


Kamar yadda kagani a photo dake sama gurin Phone No nasaka MTN Number  gurin Data Network nasaka MTN NETWORK gurin Data Bundle nasaka MTN - 1GB - N453 idan kadanna Buy Data zasu turawa wannan lamba sannan sucire N453 daga cikin wallet dinka.

Haka abin yake aduk data daka sayarwa wani, Kamar yadda kagani asama zasu baka 1GB a N453 kaikuma zaka iya sayar dashi N500, N550 har zuwa N600 sai yadda Kake so zaka sayar. Sannan duk layin daka zaba wajen turawa data zasu nuna maka adadin farashin datan na wannan layi, Don haka zaka iya ganin farashin daban daban.


Sannan Zaka iya sayar da VTU idan kashiga inda aka rubuta VTU/Recharge shima zaka samu wani kaso idan katurawa wani amma baikai Data riba ba.Abin Lura: Shine idan kana da kudi a wallet dinka zaka iya duk wani abu dakake so a Sbu9ja ba sai iya sayen data ba, Kamar yadda nafada abaya zaka iya biyan kudin makaranta da kuma zaka sayen VTU daga wannan website da sauran abubuwa.


Iyakar abin dazan kawo muku kenan akan Yadda Ake Kasuwancin A Internet Data > VTU Recharge Card ina fatan wannan rubutu zai amfaneku kuma Don Allah kuyi share zuwa wasu gurare domin wasu suma su qaru.


Zaku Iya Join Da Shafin HausaTechs.Com Dake Facebook Click Here Kokuma Idan Kuna Da Tambaya Zaku Iya Magana Damu Ko Watsapp Da 07066870719, Mungode.

Please Share Our Post

Post a comment

0 Comments