Looking For Anything Specific?

Airtel Garabasa: Yadda Zaka Samu Kyautar 4.6GB Da N200 23GB Da N1000

Airtel Garabasa: Yadda Zaka Samu 4.6GB Da N200 23GB Da N1000

Ina masu amfani da layin Airtel musamman masu yin browsing?  to yau munzo muku da wani albishir wanda insha Allah zakuyi farin ciki idan kukaji wannan labari. 


Kamfanin kiran waya na Airtel yasha kawowa mutane garabasa masu sauki a wajen sayen data, Sai dai wannan garabasa wanda zamu nuna muku tasha bambam da sauran na baya domin ita wannan baka bukatar kashe kudi domin samunta. 


Idan Kana biye dani zan nuna maka yadda zaka samu wannan garabasa akan layinka na Airtel domin bakowane layine yake samun wannan dama ba. Idan kana so kasamu wannan garabasa dole sai kana da Airtel 4G wanda yakai wata 3 (Three Months) dayin Register kuma kada yawuce wata 3 idan yawuce haka baza kasamu wannan garabasa ba.Wato abin danake nufi shine layin Airtel 4G da akayi Register daga Wata 2 zuwa 3 shine zai samu wannan garabasa, Ina fatan kungane. 


Domin sanin kwanakin Register na layin Airtel zaka iya danna *746# akan wayarka zaka samu sako mai dauke da kwana da shekarar Register na layin Airtel, Idan layinka yakai yadda nafada abaya to zaka samu wannan dama. 


Yadda Zaka Samu Kyautar 4.6GB Da N200 23GB Da N1000 Alayin Airtel

Domin samun wannan garabasa katabbatar kasaka katin N200 akan layinka na Airtel ( Banda Transfer ) da wannan Code *126*pin# katin yana shiga zaka samu Kyautar 4.6GB batare da antaba maka N200 daka sakaba.

Idan kuma kana son samun 23GB sai kasaka katin N1000 ( Banda Transfer ) akan layinka na Airtel da Code *126*pin# yana shiga zaka samu Kyautar 23GB kuma baza adauke N1000 daka sakaba.


Da wannan garabasa zaka iya tara sama da 100GB idan kaga dama,  Abin daza kayi kawai shine kamaimaita saka katin aduk lokacin daka saka zaka samu Kyautar Data.Zaka iya duba data balance idan kadanna *140# kokuma *223# nantake zaka gani.


Wannan shine karshen wannan bayani muna fatan zaku samu wannan garabasa, Idan kunji dadin wannan post kutarashi zuwa wani guri,  Mungode.

Post a comment

0 Comments